* Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kan wannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wani mai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi.
* Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya.
* Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i (ƙarya), da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan.