* An bai wa Annabi zaɓi da ya yi hukunci ko kada ya yi, a tsakãnin kafirai biyu idan sun yarda da hukuncinsa. Wannan dãmã tana aiki a kotunan Musulmi ga abin da ya shafi haƙƙoƙi kawai, amma ga 'jara'im a ƙasar Musulmi tilas sai a bi shari'ar Musulunci domin tsaron aminci, sai dai kafiri yana iya shan giyarsa, ga misãli a ɓoye banda a cikin jama'a. Haka kuma laifuka na al'adunsu kuma Musulmi bã za su taɓa masu su ba, sai su yi hukuncinsu a tsakãninsu.