* Dõmin ku san haka kuma ku himmatu ga tsare alkawurran Sa.
* Wannan lõkacin yã nuna shiɗai ne lõkacin saukar hukunci kõwane iri ne daga Allah. Wanda ya ce Annabi yã faɗa masa wani hukunci a kan wata matsala, bãyan rasuwarsa, tsĩra da aminci su tabbata gare shi, to, bã zã a karɓar masa ba, dõmin yã sãɓã wa nassin Alƙur'ãni. Kuma mafarki bã ya zama hujja, balle a ɗauke shi hukunci wanda ake yin aiki da shi. Mafarkin Annabãwa ko mafarkin da Annabãwa suka tabbatar shi ne gaskiya, saura kuma sai abin da ya bayyana, kuma bai sãɓã wa sharĩa ba.
* Bahĩra da sã'iba da hãmi sunãyen dabbõbi ne waɗanda ake bari dõmin tsãfi Bukhãri yã ruwaito daga Sa'ĩd ɗan Musayyab Ya ce: "Bahĩra ita ce rãƙumar da ake hana nõnõnta dõmin aljannu, bãbu mai tãtsar ta daga mutãne. Sã'iba kuma sunã 'yanta ta dõmin gumãka, ba a ɗaukar kõme a kanta. Kuma wasĩla ita ce rãƙuma budurwa wadda ta fãra haifuwar mace, a ciki na farko, sa'an nan kuma na biyu haka mace. Suna barin ta ga gumãka idan ta sãdar da rãƙuma mata biyu bãbu namiji a tsakãninsu. Hãmi kuwa shĩ ne ƙaton rãƙumi wanda ya yi barbara shekaru sanannu a wurinsu. Idan ya ƙãre sai su bar shi ga gumãka, bã a aza kõme a kansa. Kuma waɗannan dabbõbin duka, mãsu hidimar gumãkan, su ne suke cin su.".