* Wanda yake son Ya gyãra wani sai ya gyãra kansa daga farko. Wanda ya gyara kansa ɓatar wani bã ta cutarsa. Ba a nufin a bar wa'azi wãtau a ƙyãle mutane da jãhilcinsu.
* Idan husuma ta auku a tsakãnin Musulmi da tsakãnin kãfirai, kuma su kãfiran suka zama mudda'a alaihim (waɗanda ake tuhuma), kuma bãbu wata shaida sai su, to, sai su yi rantsuwa a wurin ibãdarsu, a kan su ne da gaskiya, a hukumta musu da hakkin. Bayan haka, idan an sãmi wata shaida a kan ƙaryarsu ana warware hukuncin a bãyan mudda'i (mãsu ƙãra) biyu Musulmi sun yi rantsuwa cewa abin da waɗancan suka faɗa ƙarya ne, abin da shaidunsu suka yi shaida da shi, shi ne gaskiya.