పవిత్ర ఖురాన్ యొక్క భావార్థాల అనువాదం - హౌసా అనువాదం - అబూ బక్ర్ జూమీ

పేజీ నెంబరు: 121:106 close

external-link copy
84 : 5

وَمَا لَنَا لَا نُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَا جَآءَنَا مِنَ ٱلۡحَقِّ وَنَطۡمَعُ أَن يُدۡخِلَنَا رَبُّنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلصَّٰلِحِينَ

"Kuma mene ne yake gare mu, bã zã mu yi ĩmãni daAllah ba, da kuma abin da ya zo mana daga gaskiya, kuma munã gurin Ubangijinmu Ya shigar da mu tãre da mutãne sãlihai?" info
التفاسير:

external-link copy
85 : 5

فَأَثَٰبَهُمُ ٱللَّهُ بِمَا قَالُواْ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Sabõda haka, Allah Yã sãkã musu, dõmin abin da suka faɗa da gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu, kuma wannan ne sakamakon mãsu kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
86 : 5

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Kuma waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, waɗancan ne abõkan Wuta. info
التفاسير:

external-link copy
87 : 5

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحَرِّمُواْ طَيِّبَٰتِ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكُمۡ وَلَا تَعۡتَدُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُعۡتَدِينَ

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.* info

* Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kan wannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wani mai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi.

التفاسير:

external-link copy
88 : 5

وَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ

Kuma ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, halat mai daɗi, kuma ku bi Allah da taƙawa, wanda yake ku, mãsu ĩmãni ne da shi. info
التفاسير:

external-link copy
89 : 5

لَا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا عَقَّدتُّمُ ٱلۡأَيۡمَٰنَۖ فَكَفَّٰرَتُهُۥٓ إِطۡعَامُ عَشَرَةِ مَسَٰكِينَ مِنۡ أَوۡسَطِ مَا تُطۡعِمُونَ أَهۡلِيكُمۡ أَوۡ كِسۡوَتُهُمۡ أَوۡ تَحۡرِيرُ رَقَبَةٖۖ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖۚ ذَٰلِكَ كَفَّٰرَةُ أَيۡمَٰنِكُمۡ إِذَا حَلَفۡتُمۡۚ وَٱحۡفَظُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa* a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa 'yantãwar wuya. Sa'an nan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa. info

* Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya.

التفاسير:

external-link copy
90 : 5

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡخَمۡرُ وَٱلۡمَيۡسِرُ وَٱلۡأَنصَابُ وَٱلۡأَزۡلَٰمُ رِجۡسٞ مِّنۡ عَمَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَٱجۡتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a*, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara. info

* Yin cãca da shan giya da refu da kiban ƙuri'a, aikatar da su warware alkawari ne na hana cin dukiyar mutãne da bãɗi1i (ƙarya), da tsaron salla da Allah Ya yi umurni a tsare; watau rashin taƙawa ke nan.

التفاسير: