* Rantsuwa alkawari ce da sunãn Allah, cewa mai rantsuwar zai aikata ko kuwa bã zai aikata ba, kõ kuwa a kan tabbatar wani abu a kan sifar da ya ambata, kõ kuwa kõruwarsa daga wannan sifar. Wanda ya yi rantsuwa sa'an nan ya yi hinsi, to, sai ya yi kaffãra, kamar yadda aka ambata a cikin ãyar. Sai fa idan ta zama yãsassar rantsuwa ce, wadda mutum ya yi a kan saninsa, sa'an nan sanin nan ya warware, sabõda bayyanar wani abu. Wasu sun ce ita ce rantsuwar da ake yi a cikin magana bã da nufi ba, kamar ã'a wallãhi, ko ĩ, wallãhi. Kuma akwai rantsuwar gamusa a kan ƙarya. Ita ma bãbu kaffãra sabõda ita, sai tuba zuwa ga Allah da istigfãri, kuma tanã sanya tsiya.