Përkthimi i kuptimeve të Kuranit Fisnik - Përkthimi në gjuhën hausa - Ebubekër Xhumi

Numri i faqes:close

external-link copy
257 : 2

ٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّٰغُوتُ يُخۡرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَٰتِۗ أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne. info
التفاسير:

external-link copy
258 : 2

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِي حَآجَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ فِي رَبِّهِۦٓ أَنۡ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ إِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّيَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحۡيِۦ وَأُمِيتُۖ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأۡتِي بِٱلشَّمۡسِ مِنَ ٱلۡمَشۡرِقِ فَأۡتِ بِهَا مِنَ ٱلۡمَغۡرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِي كَفَرَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ

Shin, ba ka gani* ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai. info

* Ƙissar farko ta Ibrãhĩm da Namarũzu.

التفاسير:

external-link copy
259 : 2

أَوۡ كَٱلَّذِي مَرَّ عَلَىٰ قَرۡيَةٖ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحۡيِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِاْئَةَ عَامٖ ثُمَّ بَعَثَهُۥۖ قَالَ كَمۡ لَبِثۡتَۖ قَالَ لَبِثۡتُ يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۖ قَالَ بَل لَّبِثۡتَ مِاْئَةَ عَامٖ فَٱنظُرۡ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمۡ يَتَسَنَّهۡۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجۡعَلَكَ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِۖ وَٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡعِظَامِ كَيۡفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكۡسُوهَا لَحۡمٗاۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعۡلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kõ kuwa* wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne." info

* Ƙissa ta biyu Uzairu da alƙarya matacciya, da jãkinsa, da abincinsa bãyan shekara ɗari.

التفاسير: