* Jũyãwar alƙibla abu ne na gaskiya daga Allah dõmin rarrashin wanda Allah bai yi nufi da tsĩrarsa ba ya ƙãre. Bãyan rarrashi sai yankewa wannan shi ne matakin farko da Musulmi suka fara tsiraita da shi daga maƙiyansu bayyane. Yanzu kuma Musulmi sun zama dabam.
* Jũyar da alƙibla da yankewa daga dukkan kãfirai da hani daga tsõronsu kuma Allah Ya farkar da Musulmi ga ni'imõmin da Ya yi musu game da aiko Annabi daga gare su, zuwa gare su, a cikinsu, dõmin ya tsarkake su, bayyane da ɓõye, daga dukan ƙurar kãfirci. Wannan ya nũna cewa sai an yi rarrashin mutãne wajen kira zuwa ga addini da kõwace hanya mai yiwuwa. Bãyan haka a yanke wa wanda ya ƙi bin gaskiya bayyane kuma kada a ji tsõronsa. Kuma aka umurce su da fuskanta zuwa ga Allah kawai da tunãwa gare Shi da gõdiya, da nisantar kafirci.
* Magana kuma ta fuskanta zuwa ga mũminai kawai dõmin a shirya zamansu.