* Tunãtar da Banĩ Isrã'ĩla alkawurra gõma da Allah Yã yi da Mũsã a cikin Attaura a kansu. Na farko bã zã su bauta wa kõwa ba fãce Allah. Na biyu kyautata wa iyãye da dangi da marãyu da matalauta. Na uku, faɗin magana mai kyau zuwa ga mutãne. Na huɗu, tsayar da salla. Nabiyar, bãyar da zakka. Na shida, bã zã a kashe rai bãbu hakki na sharĩ'a ba. Na bakwai, bã zã a fitar da kõwa daga gidansa ba. Na takwas, bã zã a taimaki azzãlumi a kan zãluncinsa ba. Na tara, idan abõkan gãbã sun kãma wani daga cikinsu, su yi fansarsa. Nagõma, ɗã'a ga kõwane Manzon Allah wanda bai sãɓãwa Attaura ba ga aƙida.