* Sunã cewa idan Annabin ƙarshen zãmaninsa ya zo, zã su yãƙi kãfiran Lãrabãwa da shi. Sunã zaton a cikinsu zai ɓullo. Sai ya fito a cikin Lãrabãwan.
* Bisa ga zãlunci, watau hãsada. Sun yi hãsadar Allah Ya saukar da abin da Yake so na falalarSa a kan wanda Yake so, shi ne Muhammadu, a cikin Lãrabãwa.
* Waɗannan Annabãwan da kuka kashe ko kuka ƙaryata a cikinku suke kũ ne aka saukar wa da abin da aka bã su, sabõda haka da'awarku ta cewa kunã ĩmãni da abin da aka saukar muku ƙarya ce.
* Riƙo A nan ma'anarsa bautawa; watau kõmãwa ga maraƙi da ibãda, ku bar Allah, bãyan Musa ya nuna muku ãyõyin Allah, yana ƙãra ƙaryata maganarku, ta cewa kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku kawai. Dã kunã yin ĩmãni da abin da aka saukar muku, dã waɗannan abubuwa ba su auku ba daga gare ku.
* A lõkacin da aka bã su Attaura sai suka ƙi aiki da ita sai da aka ɓamɓari dutse aka ɗaukaka shi sama a kansu, idan ba su yi aiki da ita ba ya fãɗa kansu. Sai suka karɓa, sa'an nan daga bãya kuma suka warware dõmin haka Ya ce: "Suka ce: Mun jiya kuma mun ƙiya." Hãsali dai Yahũdu sun ƙi aiki da Littãfinsu, Attaura.