แปล​ความหมาย​อัลกุรอาน​ - คำแปลภาษาเฮาซา - อบูบักร์ ญูมีย์

หมายเลข​หน้า​:close

external-link copy
253 : 2

۞ تِلۡكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۘ مِّنۡهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُۖ وَرَفَعَ بَعۡضَهُمۡ دَرَجَٰتٖۚ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخۡتَلَفُواْ فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ وَمِنۡهُم مَّن كَفَرَۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلُواْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

Waɗancan manzannin* Mun fĩfĩta sãshensu a kan sãshe: Daga cikinsu akwai wanda Allah Ya yi masa magana; kuma Ya ɗaukaka sãshensu da darajõji; kuma Muka bai wa Ĩsã dan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafã shi da Rũhi mai tsarki. Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi. info

* Allah Yanã tunkuɗe ɓarna a cikin ƙasa da wãsiɗar karantar da mãsu alheri, dõmin su yãƙi mãsu sharri. Ya saukar da ilminSa da wãsiɗar manzanninSa waɗanda Ya tabbatar da cewa Muhammadu, tsira da amincinSa su tabbata a gare shi, yana cikinsu kuma shi ne ya fi ɗaukaka daga cikinsu. Daga wannan ãyã zuwa ƙarshen Sũra duka, ƙãrin bãyani ne da shiryarwa ga hukunce-hukuncen da suka gabãta da kuma yadda zã a zartar da aiki da su, kamar yadda tsãrin magana zai nũna in Allah Ya so.

التفاسير:

external-link copy
254 : 2

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خُلَّةٞ وَلَا شَفَٰعَةٞۗ وَٱلۡكَٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّٰلِمُونَ

Ya ku waɗanda* suka yi ĩmãni! Ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gabãnin wani yini ya zo bãbu ciniki a cikinsa kuma bãbu abũta, kuma bãbu cẽto, kuma kãfirai sũ ne Azzãlumai. info

* Bãyan tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sa'an nan ya sãbunta fuskanta da kira zuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni da Annabi, kuma ya farkar da su game da zuwan babbar rãna ta Ƙiyãma. Sa'an nan ya faɗi sũnanSa Ta'ãla, Allah Mai sifõfin da ke cikin ãyã ta 255.

التفاسير:

external-link copy
255 : 2

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
256 : 2

لَآ إِكۡرَاهَ فِي ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَيِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Bãbu tĩlastãwa* a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani. info

* Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni.

التفاسير: