* Allah Yanã tunkuɗe ɓarna a cikin ƙasa da wãsiɗar karantar da mãsu alheri, dõmin su yãƙi mãsu sharri. Ya saukar da ilminSa da wãsiɗar manzanninSa waɗanda Ya tabbatar da cewa Muhammadu, tsira da amincinSa su tabbata a gare shi, yana cikinsu kuma shi ne ya fi ɗaukaka daga cikinsu. Daga wannan ãyã zuwa ƙarshen Sũra duka, ƙãrin bãyani ne da shiryarwa ga hukunce-hukuncen da suka gabãta da kuma yadda zã a zartar da aiki da su, kamar yadda tsãrin magana zai nũna in Allah Ya so.
* Bãyan tabbatar da manzancin Annabi Muhammadu tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, sa'an nan ya sãbunta fuskanta da kira zuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni da Annabi, kuma ya farkar da su game da zuwan babbar rãna ta Ƙiyãma. Sa'an nan ya faɗi sũnanSa Ta'ãla, Allah Mai sifõfin da ke cikin ãyã ta 255.
* Abũbuwan bautãwa, iri biyu ne; Ubangijin da Yã aiko Muhammadu da wannan gaskiya da shiriya Shĩ ne Allah, da sauran iyãyen giji mãsu dõkõkin kai da na son zũkãta kamar nafsu da Shaiɗan, na aljannu da mutãne, mãsu ƙãga abin da suke so, su ƙira mutane a kansa ana ce musu Ɗãgũtu. Ya yi bayãnin sakamakon mabiyin kõwane irin bautawar. Sa'an nan ya biyar da ƙissõshi uku dõmin bayãnin abin da wannan magana ta ƙunsa; ta farko Namarũzu tãre da Ibrãhĩm, tanã nũna cewa mai mulki anã umurtar sa da bin Allah da taƙawa, idan ya bi son zũciyarsa, to, ya zama Ɗãgũtu. Allah zai halakar da shi. Ta biyu ƙissar Uzairu, tanã nũna cewa bãbu abin da yake da wuya ga Allah. Ta uku ƙissar Ibrãhim da yadda Allah ke rãyar da matattu, tanã nũna cewa bãbu laifi ka roƙi Allah Ya gãnar da kai dukan abin da ya shige maka duhu dõmin ka ƙãrã ĩmãni.