* Kashi na biyu daga cikin jama'a sũ ne kãfiran da suka dõge akan kãfircin su, babu wani gisshi kuma Allah Yã san bã zã su musulunta ba.
* Kashi na uku su ne munãfukai da suka bayyana Musulunci da bãki amma zuciyarsu tanã a kan kãfirci.
* Kashi na hudu su ne Yahudãwa waɗanda suke sun san gaskiyar Annabcin Muhammadu da Manzancinsa, amma hãsada ta hana su su bi shi, sunã ƙõƙãrin ɓãta abin da ya zo da shi ta hanyar jħfa shibhõhi a ciki, dõmin su kange mutãne daga shigarsa. Sabõda haka aka ce musu shaiɗãnu. Duk wanda ya san gaskiya amma kuma ya yi girman kai daga binta, to, shi ne shaiɗan, daga aljannu kõ daga mutane.