Përkthimi i kuptimeve të Kuranit Fisnik - Përkthimi në gjuhën hausa - Ebubekër Xhumi

Numri i faqes:close

external-link copy
19 : 6

قُلۡ أَيُّ شَيۡءٍ أَكۡبَرُ شَهَٰدَةٗۖ قُلِ ٱللَّهُۖ شَهِيدُۢ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ لِأُنذِرَكُم بِهِۦ وَمَنۢ بَلَغَۚ أَئِنَّكُمۡ لَتَشۡهَدُونَ أَنَّ مَعَ ٱللَّهِ ءَالِهَةً أُخۡرَىٰۚ قُل لَّآ أَشۡهَدُۚ قُلۡ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ وَإِنَّنِي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

Ka ce: "Wane abu ne mafi girma ga shaida?" Ka ce: "Allah ne shaida a tsakãnina da tsakaninku. Kuma an yiwo wahayin wannan Alƙur'ãni dõmin in yi muku gargaɗi da shi, da wanda lãbãri ya kai gare shi. Shin lalle ne ku, haƙĩƙa, kunã shaidar cẽwa, lalle ne tãre da Allah akwai wasu abũbuwan bautawa?" Ka ce: "Bã zan yi shaidar (haka) ba." Ka ce: "Abin sani, Shi ne Abin bautãwa Guda kumã lalle ne nĩ barrantacce ne daga abin da kuke yi na shirka" info
التفاسير:

external-link copy
20 : 6

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمُۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa* kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni. info

* Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: "Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.".

التفاسير:

external-link copy
21 : 6

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّٰلِمُونَ

Wãne ne mafi zãlunci daga wanda yake ƙirƙira karya ga Allah, kõ kuwa ya ƙaryata game da ãyõyinsa? Lalle ne shĩ, azzalumai bã zã su ci nasara ba. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 6

وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَيۡنَ شُرَكَآؤُكُمُ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ

Kuma rãnar da Muka tãra su gabã ɗaya, sa'an nan Mu ce wa waɗanda suka yi shirki: "Inã abõkan tãrayyarku waɗanda kuka kasance kunã riyãwa?" info
التفاسير:

external-link copy
23 : 6

ثُمَّ لَمۡ تَكُن فِتۡنَتُهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ وَٱللَّهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا مُشۡرِكِينَ

Sa'an nan kuma fitinarsu ba ta kasance ba, fãce dõmin sun ce: "Munã rantsuwa da Allah Ubangijinmu, ba mu kasance mãsu yin shirki ba." info
التفاسير:

external-link copy
24 : 6

ٱنظُرۡ كَيۡفَ كَذَبُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡۚ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Ka dũba yadda suka ƙaryata kansu! Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙira ƙaryarsa, ya ɓace daga gare su. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 6

وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَۖ وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوكَ يُجَٰدِلُونَكَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Kuma daga cikinsu akwai wanda yake saurãre gare ka. Kuma Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi. Kuma idan sun ga kõwace ãyã bã zã su yi ĩmãni da ita ba har idan sunjẽ maka sunã jãyayya da kai, waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Wannan bai zama ba fãce tãtsũniyõyin mutãnen farko." info
التفاسير:

external-link copy
26 : 6

وَهُمۡ يَنۡهَوۡنَ عَنۡهُ وَيَنۡـَٔوۡنَ عَنۡهُۖ وَإِن يُهۡلِكُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Kuma sunã hanãwa daga gare shi, kuma sunã nĩsanta daga gare shi, kuma bã su halakarwa, fãce kansu, kuma bã su sansancẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 6

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَى ٱلنَّارِ فَقَالُواْ يَٰلَيۡتَنَا نُرَدُّ وَلَا نُكَذِّبَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma dã kanã gani, a lõkacin da aka tsayar da su a kan wuta, sai suka ce: "Yã kaitõnmu! Dã ana mayar da mu, kuma bã zã mu ƙaryata ba daga ãyõyin Ubangijinmu, kuma zã mu kasance Daga mũminai." info
التفاسير: