* Wahayin shaiɗãnu sãshensu zuwa ga sãshe da ƙãwata ƙarya ta zama kamar gaskiya. Kamar Shaiɗan ya sanya wasiwãsi: Dã da'awar Annabi gaskiya ce: Ai dã manyan mutãne ne zã su fãra bin ta, ba matalautã ba, kõ kuwa annabi mai sihiri ne dõmin yanã raba miji da mãta, da ɗa da uba. Watau su karkatar da magana, dõmin su karkatar da wãwãye daga bin gaskiya.
* Musulunci kõ Alƙur'ãni ne cikon addinin Allah, babu mai iya zõwa da wani abu sãbo kõ ya ƙãra wani abu a cikin sa ta kõwace hanya kuma bãbu mai iya musanya wani abu a cikinsa. Ya cika ya kammala, sai biya kawai. Annabi ya ce: "Wanda ya yi wani aiki ba da umuruinsa a kan abin da ya aikata ɗin nan ba, to, an mayar masa; ba a karɓaba.".
* Kamar maganarsu cewa mũshe wanda Allah da kansa Ya kashe, ya fi dã cewa da a ci shi, bisa ga abin da mutãne suka yanka.
* An sani daga nan cewa ambaton sũnan Allah wajen yankan dabba wãjibi ne, idan an tuna. Wanda ya manta, anã cin yankansa, amma wanda ya bari da gangan, bã zã a ci yankansa ba.