* Zuwan malã'iku dõmin karɓar rãyukansu, zuwan Allah dõmin yin hisãbin bãyi, zuwan sãshen ãyõyin Ubangiji shĩ ne fitõwar rãnã daga yamma da fitar Rãƙumar Sãlihu. Waɗannan abũbuwa duka idan sun auku a kan wanda bã shi da imani a gabãnin aukuwarsu, kuma ya zama yã aikata ayyukan alheri da shari'a ta umurce shi da yi, to, bã za a karɓi wani ĩmãninsa ba.
* Bãyan bayãnin wanda bai yi ĩmani ba sai bayãnin sababin rashin karɓar ĩmãnin ya zo, sai kuma ya ci gaba da bayãnin cewa, kõ wanda ya yi ĩmãnin idan yã ƙãra wasa abũbuwa a cikin addĩni bisa ga abin da Allah Ya saukar, ta haka har mutane suka zama ƙungiya ƙungiya, kamar mãsu ɗarĩƙõƙi na tasawwufi, to, su ma Annabi bã ya tãre da su ga kõme dõmin sun kõma wa hanyar jahiliyya a lõkacin da wasu suke ƙãga hukunce-hukunce a kan mutãne, suka zama da yin haka nan abũbũwan bautãwa, kuma mãsu bin su suka zama mushirikai. Daga nan har zuwa ga ƙarshen sũrar duka ta'lĩƙi ne ga dukan abin da sũrar ta ƙunsa na tauhĩdin Rubũbiyya da taƙaitãwa ga bãyanin muhimman mas'alolin da ta ƙunsa. Saninta shi ne rũhin Addini.