د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
49 : 2

وَإِذۡ نَجَّيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ

Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku. info
التفاسير:

external-link copy
50 : 2

وَإِذۡ فَرَقۡنَا بِكُمُ ٱلۡبَحۡرَ فَأَنجَيۡنَٰكُمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ

Kuma a lõkacin da Muka raba tẽku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir'auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo. info
التفاسير:

external-link copy
51 : 2

وَإِذۡ وَٰعَدۡنَا مُوسَىٰٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ

Kuma a lõkacin da muka yi wa'adi ga Mũsa, dare arba'in, sa'an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa). info
التفاسير:

external-link copy
52 : 2

ثُمَّ عَفَوۡنَا عَنكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Sa'an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
53 : 2

وَإِذۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡفُرۡقَانَ لَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabẽwa, tsammãninku, kuna shiryuwa. info
التفاسير:

external-link copy
54 : 2

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِنَّكُمۡ ظَلَمۡتُمۡ أَنفُسَكُم بِٱتِّخَاذِكُمُ ٱلۡعِجۡلَ فَتُوبُوٓاْ إِلَىٰ بَارِئِكُمۡ فَٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ عِندَ بَارِئِكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
55 : 2

وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نُّؤۡمِنَ لَكَ حَتَّىٰ نَرَى ٱللَّهَ جَهۡرَةٗ فَأَخَذَتۡكُمُ ٱلصَّٰعِقَةُ وَأَنتُمۡ تَنظُرُونَ

Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo. info
التفاسير:

external-link copy
56 : 2

ثُمَّ بَعَثۡنَٰكُم مِّنۢ بَعۡدِ مَوۡتِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Sa'an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
57 : 2

وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡغَمَامَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta. info
التفاسير: