Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir'auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.
Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafii alheri a wajen mahaliccinku. Sa'an nan Ya karɓi tuba a kanku. lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.
Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.