* Abũbuwan da aka hana, a cikin azumi, da ranã, an halatta su da dare har zuwa fitar alfijiri wato sĩlĩli fari na hasken sãfiya da sĩlĩli baƙi na duhun dare. Bã a yin jima'i kõ da dare a hãlin itikãfi, kuma bã a yin itikãfi sai a cikin masallãci.
* Haramun ne cin dũkiyar mutãne da zãlunci. An haɗa wannan ãyã da ta gabãninta, ta azumi, dõmin haɗin hana ci da ya gama su. Sãduwa da mahukunta da dukiya, shi ne rashawa, Allah Yã la'ani mai bãyar da ita da mai karɓarta.
* Shiga Musulunci yarda ne da barin al'ãdu da hukunce-hukuncen jãhiliyya, sabõda haka ake sãmun tambayõyi da yawa daga sãbon Musulmi kãfin ya kammala da canza tsõfaffin al'ãdunsa da sãbabbi. Allah Yã yi tarbiyar Sahabban Annabi a cikin rãyuwar Annabi, bãyan saukar wahayi.
* An umurci Musulmi da tsare kansu da yãƙi ga duk wanda ya yãƙe su, a kõ'ina yake. Sai dai an hana su tsõkanar wasu, kuma an hana su su yi yãƙi a cikin Hurumin Makka sai fa idan an fãɗa su da yãƙi a cikinsa.