د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
177 : 2

۞ لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَٰهَدُواْۖ وَٱلصَّٰبِرِينَ فِي ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِۗ أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ

Bai zama addini* ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa, kuma ya bãyar da dũkiya, akan yana son ta, ga mai zumunta da marãyu da matalauta da ɗan hanya da mãsu rõƙo, kuma a cikin fansar wuya, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bãyar da zakka, da mãsu cika alkawari idan sun ƙulla alkawarin da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi. Waɗannan su ne suka yi gaskiya. Kuma waɗannan su ne mãsu taƙawa. info

* Bayãnin cewa Musulunci bã yin salla ɗai ba ne. A'aha! Musulunci tsarewar rãyuwane kamar yadda Allah Ya ce a tsare ta.

التفاسير:

external-link copy
178 : 2

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِي ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِيَ لَهُۥ مِنۡ أَخِيهِ شَيۡءٞ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَٰنٖۗ ذَٰلِكَ تَخۡفِيفٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٞۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta, a kanku, yin ƙisãsi* a cikin kasassu. ɗa da ɗa kuma bãwa da bãwa, kuma mace da mace, to, wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga ɗan'uwansa to a bi da alhẽri da biya zuwa gare, shi da kyautatãwa. Wancan sauƙaƙewa ne daga Ubangijinku, kuma rahama ce. To, wanda ya yi zãlunci a bãyan wancan, to, yana da azãba mai raɗaɗi. info

* Bayãnin hukuncin ƙisãsi: Ana kashe namiji sabõda ya kashe mace, bã a kashe ɗa da Musulmi saboda kashin bãwa da kãfiri sai idan ya zama kisan gila ne kõ ƙwãce. Gila shĩ ne kashe mutum dõmin dũkiyarsa kõ mãtarsa.

التفاسير:

external-link copy
179 : 2

وَلَكُمۡ فِي ٱلۡقِصَاصِ حَيَوٰةٞ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
180 : 2

كُتِبَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ إِن تَرَكَ خَيۡرًا ٱلۡوَصِيَّةُ لِلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma an wajabta,* a kanku idan mutuwa ta halarci ɗayanku, idan ya bar wata dũkiya, wasiyya dõmin mahaifa da dangi bisa ga abin da aka sani; wajabce a kan mãsu taƙawa. info

* Bayãnin hukuncin wasiyya: Sunna ta bayyana cewa bãbu wasiyya ga wanda zai yi gãdo, kuma wasiyya bã zã ta shige sulusin dũkiyar tarika ba.

التفاسير:

external-link copy
181 : 2

فَمَنۢ بَدَّلَهُۥ بَعۡدَ مَا سَمِعَهُۥ فَإِنَّمَآ إِثۡمُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يُبَدِّلُونَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

To, wanda ya musanya masa a bãyan ya ji shi, to, kawai laifinsa yana a kan waɗanda suke musanya shi. Lalle ne, Allah Mai ji ne, Masani. info
التفاسير: