د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
120 : 2

وَلَن تَرۡضَىٰ عَنكَ ٱلۡيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمۡۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ ٱلَّذِي جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ

Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aƙidarsu. Ka ce: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya." Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majiɓinci, kuma bãbu wani mataimaki. info
التفاسير:

external-link copy
121 : 2

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَتۡلُونَهُۥ حَقَّ تِلَاوَتِهِۦٓ أُوْلَٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Waɗanda Muka bai wa Littãfi suna karãtunsa a kan haƙƙin karãtunsa, waɗannan suna ĩmani da shi (Alƙur'ãni). Kuma wanda ya kãfirta da shi, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra. info
التفاسير:

external-link copy
122 : 2

يَٰبَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَنِّي فَضَّلۡتُكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku* tuna ni'imaTa wadda Na ni'imtar da ita a kanku, kuma lalle ne Nĩ, Nã fĩfĩtã ku a kan tãlikai. info

* Kira na ƙarshe zuwa ga Yahũdu dõmin shiga Musulunci. An biyar da gargaɗi gare su da tunãtar da su cewa wannan addinin fa, shi ne addinin kãkansu Ibrãhim, dõmin kada su fanɗare daga addinin ubanninsu na ƙwarai. Kuma sunã da lãbãrin ginin Ɗakin Ka'aba da addu'ar da lbrahim ya yi alõkacin, wadda ta ƙunshi zuwan annabi daga cikin zuriyar Isama'ila a Makka, watau Fãrãna.

التفاسير:

external-link copy
123 : 2

وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Ku ji tsõron wani yini, (a cikinsa) wani rai bã ya tunkuɗe wa wani rai kõme kuma bã a karɓar fansa daga gare shi, kuma wani cẽto bã ya amfanin sa, kuma ba su zama ana taimakon su ba. info
التفاسير:

external-link copy
124 : 2

۞ وَإِذِ ٱبۡتَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ رَبُّهُۥ بِكَلِمَٰتٖ فَأَتَمَّهُنَّۖ قَالَ إِنِّي جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامٗاۖ قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِيۖ قَالَ لَا يَنَالُ عَهۡدِي ٱلظَّٰلِمِينَ

Kuma a lõkacin da Ubangijin Ibrãhim Ya jarrabẽ shi da wasu kalmõmi, sai ya cika su. Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Mai sanya ka shugaba dõmin mutãne ne." Ya ce: "Kuma daga zũriyata." Ya ce: "AlkawarĩNa bã zai sãmu azzãlumai ba." info
التفاسير:

external-link copy
125 : 2

وَإِذۡ جَعَلۡنَا ٱلۡبَيۡتَ مَثَابَةٗ لِّلنَّاسِ وَأَمۡنٗا وَٱتَّخِذُواْ مِن مَّقَامِ إِبۡرَٰهِـۧمَ مُصَلّٗىۖ وَعَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡعَٰكِفِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ

Kuma a lõkacin da Muka sanya ¦ãkin ya zama makõma ga mutãne, da aminci, kuma ku riƙi wurin salla daga Maƙãmi Ibrãhĩm, kuma Muka yi alƙawari zuwa ga Ibrãhĩm, da Ismã'ila da cẽwa: "Ku tsarkake ¦ãkiNa dõmin mãsu ɗawãfi da mãsu lizimta da mãsu rukũ'i, mãsu sujada." info
التفاسير:

external-link copy
126 : 2

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا بَلَدًا ءَامِنٗا وَٱرۡزُقۡ أَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنۡ ءَامَنَ مِنۡهُم بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلٗا ثُمَّ أَضۡطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma a lõkacin da lbrãhĩm ya ce: "Yã Ubangijĩna! Ka sanya wannan gari amintacce, Ka azurta mutãnensa, daga 'ya'yan itãcen, wanda ya yi ĩmãni, daga gare su, da Allah da Ranar Lãhira." Allah Ya ce: "Wanda ya kãfirta ma Ina jiyar da shi dãɗi kaɗan, sa'an nan kuma Ina tĩlastã shi zuwa ga azãbar Wuta. Kuma makõmar, ta munana." info
التفاسير: