Traducción de los significados del Sagrado Corán - Traducción al idioma hausa- Abu Bakr Jomy

Al'taubah

external-link copy
1 : 9

بَرَآءَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Barranta daga Allah da Manzon Sa zuwa ga waɗan da kuka yi wa Alkawari daga mãsu shirki* info

* Kãfirai iri uku ne: mãsu addinin al'ãda kamar Lãrabãwa sũ ne mãsu shirki, sa'an nan mãsu bin Littãfi shãfaffe watau Yahudu da Nasãra sa'an nan da munãfukan wannan al'umma. Ya fãra da mãsu shirki da bayãnin irin ayubansu, sa'an nan ya yi bayãnin sauran kamar haka.

التفاسير:

external-link copy
2 : 9

فَسِيحُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُخۡزِي ٱلۡكَٰفِرِينَ

Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu,* kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai. info

* Bãyan yanke sulhu, Allah Yabai wa kãfirai watã huɗu na amãna, dõmin su ƙãre harkõkinsu da wasu ma'amalõli da suka ƙulla tãre da Musulmi, sa'an nan yãƙi ya tãshi. Anã nufin mãsu addinin al'ãda na shirki a nan.

التفاسير:

external-link copy
3 : 9

وَأَذَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلنَّاسِ يَوۡمَ ٱلۡحَجِّ ٱلۡأَكۡبَرِ أَنَّ ٱللَّهَ بَرِيٓءٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ وَرَسُولُهُۥۚ فَإِن تُبۡتُمۡ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Kuma da yẽkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cẽwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 9

إِلَّا ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ثُمَّ لَمۡ يَنقُصُوكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَمۡ يُظَٰهِرُواْ عَلَيۡكُمۡ أَحَدٗا فَأَتِمُّوٓاْ إِلَيۡهِمۡ عَهۡدَهُمۡ إِلَىٰ مُدَّتِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ

Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa'an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjẽjẽyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 9

فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلۡأَشۡهُرُ ٱلۡحُرُمُ فَٱقۡتُلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡ وَخُذُوهُمۡ وَٱحۡصُرُوهُمۡ وَٱقۡعُدُواْ لَهُمۡ كُلَّ مَرۡصَدٖۚ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmẽ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 9

وَإِنۡ أَحَدٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ٱسۡتَجَارَكَ فَأَجِرۡهُ حَتَّىٰ يَسۡمَعَ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ أَبۡلِغۡهُ مَأۡمَنَهُۥۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡلَمُونَ

Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa'an nan ka isar da shi ga wurin amincewar sa. Wan can fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗan da ba su sani ba. info
التفاسير: