* Tun farkon zuwan Annabi a Madĩna mũnafukai sun yi ta yin kaidi dõmin su ɓãta al'amarin Annabi da Musulunci, suka kãsa, har gaskiya ta bayyana, suka kãma bakinsu dõmin rashin abin da zã su iya faɗã a yarda da shi.
* Kuma a yanzu ga yãƙin Tabũka (munafukai) sun bayyana da irin uzurran da suke kãwowa dõmin kada su fita kamar mai cewa" To, Allah Ya hana zina, idan na fita nã gã mãtan Rũmãwa, bã zan iya yin haƙuri daga barinsu ba' sabõdahaka inã son a karbi uzurina kada a jefa ni a cikin fitina." Bai sani ba. da wannan rashin fitar ya jefa kansa a cikin fitinar. Dõmin zã a bar shi tãre da mãtã, sũ da shi kawai.
* Ɗayan abũbuwa biyu mãsu kyau, sũ ne mutuwa a kan shahãda kõ rinjaya da sãmun ganĩma da izza.