* Sa'an nan kuma ya bayyanã a cikin wannan ãyã ta 112 siffõfin muminai waɗanda aka fuskantar da kiran neman ciniki da su.
* Bayãnin umurni da yanke wa kãfirai, kõ da sun mutu, da barin yi musu addu'ar alheri.
* Wannan ãyã tanã nũna cewa taklĩfin da Allah Yake azã wa bãyinSa na yãƙi da waninSa, bã dõmin ya wahalar da su ba ne. Yanã yi ne dõmin alheri a gare su, Shĩ Allah Mawãdaci ne, Yanã da ƙasa da sammai, kuma shĩ ne Mai yin halittar kõme.
* Yã fãra gabãtar da cewa, "Allah Yã karɓi tũbar Annabi da waɗanda Ya ambata tãre da shi," dõmin ya biyar ãyar da ke zuwa ta tũbar waɗanda suka yi zamansu, bã da wani uzuri ba, kuma sũ bã munãfuƙai ba, aka jinkirtar da maganar tũbarsu har a bãyan hõron kwãna hamsin bãbu mai yi musu magana, bisa hanin Allah. Kuma dã an ambaci karɓar tũbarsu kawai bã da an gabãtar da tũbar waɗanda suka fita ba, dã sai a ce sun fi waɗanda suka fita, dõmin an yi nassi a kan tũbarsu. Wanda aka yi nassi akan tũbarsa, yã fi wanda. aka bari a cikin duhu.