* Kãfirai iri uku ne: mãsu addinin al'ãda kamar Lãrabãwa sũ ne mãsu shirki, sa'an nan mãsu bin Littãfi shãfaffe watau Yahudu da Nasãra sa'an nan da munãfukan wannan al'umma. Ya fãra da mãsu shirki da bayãnin irin ayubansu, sa'an nan ya yi bayãnin sauran kamar haka.
* Bãyan yanke sulhu, Allah Yabai wa kãfirai watã huɗu na amãna, dõmin su ƙãre harkõkinsu da wasu ma'amalõli da suka ƙulla tãre da Musulmi, sa'an nan yãƙi ya tãshi. Anã nufin mãsu addinin al'ãda na shirki a nan.