* Allah Ya umurci Annabi da ya bar gaggãwar karatun Alƙur'ãni a lõkacin da ake yin wahayinsa zuwa gare shi, dõmin kada ya wahala dõmin sũrar tanã karantar da cewa addinin Musulunci sauƙi ne, bai zo dõmin ya wahalar ba. Kuma tsõron yin kuskure yanã sanya yin kuskure mai jãwo wahala kamar yadda Ãdamu ya yi gaggãwar ga tsoron umurnin Allah, sai ya yi mantuwa, ya yi abin da aka hana shi har masifa ta sãmu aka fitar da shi daga Aljanna.
* Anã farkar da ɗiyan Ãdamu ga maƙiyin ubansu wanda ya sabbaba musu wahalar zuwa dũniya da haɗuwa da taklĩfi a cikinta. Kuma bin wannan taklĩfi yanã zame masa sauƙi idan sun bĩ shi yadda Allah Ya ce: amma idan sun bi hanyar Shaiɗan, maƙiyinsu, to, bãbu abin da zai sãmu a gare su fãce ƙãrin wahala daga dũniya har Lãhira.
* Wanda ya bijire daga ãyõyin Allah, shĩ ne kãfirin da bai yarda da shiga Musulunci ba.