Përkthimi i kuptimeve të Kuranit Fisnik - Përkthimi në gjuhën hausa - Ebubekër Xhumi

Daha

external-link copy
1 : 20

طه

T,H. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 20

مَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ لِتَشۡقَىٰٓ

Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 20

إِلَّا تَذۡكِرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰ

Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 20

تَنزِيلٗا مِّمَّنۡ خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ وَٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلۡعُلَى

(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 20

ٱلرَّحۡمَٰنُ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ ٱسۡتَوَىٰ

Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi. info

* Allah Ya daidaitu a kan Al'arshi daidaita wadda ta dãce da shi.

التفاسير:

external-link copy
6 : 20

لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَمَا تَحۡتَ ٱلثَّرَىٰ

Abin da yake a cikin sammai nãsa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 20

وَإِن تَجۡهَرۡ بِٱلۡقَوۡلِ فَإِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخۡفَى

Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 20

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ

Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 20

وَهَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ

Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? info
التفاسير:

external-link copy
10 : 20

إِذۡ رَءَا نَارٗا فَقَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِقَبَسٍ أَوۡ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدٗى

A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar." info
التفاسير:

external-link copy
11 : 20

فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ يَٰمُوسَىٰٓ

Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!" info
التفاسير:

external-link copy
12 : 20

إِنِّيٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخۡلَعۡ نَعۡلَيۡكَ إِنَّكَ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوٗى

"Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka* Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa." info

* An ce wa Mũsã ya ɗebe takalmansa dõmin sunã da najasa kõ kuwa sũ kansu najasa ne dõmin ya shiga wuri mai tsarki wanda ake kira Ɗuwa a cikin sahãrar Sina'i a tsakãnin Masar da Madyana.".

التفاسير: