* Dã an bã su lõkaci mai tsawo sunã jin dãɗi da rãyuwar dũniya a cikinsa, to, rãnar da mutuwa kõ azãbar Allah ta je gare su, wannan lõkacin bã zai tunkuɗe mutuwar kõ azabar ba daga gare su.
* Ka zama mai tausayi ga mũminai waɗanda suka bĩ ka, ka yi musu kamar yadda kãzã take yi wa 'ya'yanta ƙanana a lõkacin sanyi, kõ kuwa idan zã su yi barci dõmin ta kãre su daga cũta.
* Wannan dõmin raddi ne gamãsu cewa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah.