د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
207 : 26

مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يُمَتَّعُونَ

Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su. info

* Dã an bã su lõkaci mai tsawo sunã jin dãɗi da rãyuwar dũniya a cikinsa, to, rãnar da mutuwa kõ azãbar Allah ta je gare su, wannan lõkacin bã zai tunkuɗe mutuwar kõ azabar ba daga gare su.

التفاسير:

external-link copy
208 : 26

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ

Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
209 : 26

ذِكۡرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba. info
التفاسير:

external-link copy
210 : 26

وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ

Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba. info
التفاسير:

external-link copy
211 : 26

وَمَا يَنۢبَغِي لَهُمۡ وَمَا يَسۡتَطِيعُونَ

Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa. info
التفاسير:

external-link copy
212 : 26

إِنَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّمۡعِ لَمَعۡزُولُونَ

Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne. info
التفاسير:

external-link copy
213 : 26

فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ

Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba. info
التفاسير:

external-link copy
214 : 26

وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ

Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci. info
التفاسير:

external-link copy
215 : 26

وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai. info

* Ka zama mai tausayi ga mũminai waɗanda suka bĩ ka, ka yi musu kamar yadda kãzã take yi wa 'ya'yanta ƙanana a lõkacin sanyi, kõ kuwa idan zã su yi barci dõmin ta kãre su daga cũta.

التفاسير:

external-link copy
216 : 26

فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ

Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
217 : 26

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
218 : 26

ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ

Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye. info
التفاسير:

external-link copy
219 : 26

وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّٰجِدِينَ

Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada. info
التفاسير:

external-link copy
220 : 26

إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani. info

* Allah Shi ne Mai ji, ji na gaskiya, kuma Masani, sani na gaskiya.

التفاسير:

external-link copy
221 : 26

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ

Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka? info

* Wannan dõmin raddi ne gamãsu cewa aljannu ke gayawa Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Alƙur'ãni. Aljannu bã su saukã sai ga maƙaryaci, mai zunubi' Muhammadu kuwa bã haka yake ba. Sabõda haka shi bã mahaukaci ba, kuma ba wanda aljannu suke gaya wa ba. Dukan abin da ya faɗa, to, wahayi ne daga Allah.

التفاسير:

external-link copy
222 : 26

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ

Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi. info
التفاسير:

external-link copy
223 : 26

يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ

Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne. info
التفاسير:

external-link copy
224 : 26

وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ

Kuma mawãƙa* halakakku ne ke bin su. info

* Siffõfin mawãƙa sun nũna cewa Annabi Muhammadu bã mawãƙi ba ne, dõmin bã shi da ɗaya daga cikin siffõfin mawãƙa. Kuma mabiyansa ba halakakku ba ne.

التفاسير:

external-link copy
225 : 26

أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٖ يَهِيمُونَ

Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba? info
التفاسير:

external-link copy
226 : 26

وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ

Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa? info
التفاسير:

external-link copy
227 : 26

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٖ يَنقَلِبُونَ

Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa. info
التفاسير: