د قرآن کریم د معناګانو ژباړه - هوساوي ژباړه - ابو بکر ګومي

د مخ نمبر:close

external-link copy
84 : 26

وَٱجۡعَل لِّي لِسَانَ صِدۡقٖ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ

"Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe." info

* Harshen gaskiya shĩ ne yabõ mai kyau. Mutãnen ƙarshe sũ ne Musulmi al'ummar Annabi Muhammadu, mãsu shaida ga annabawa da iyar da manzanci

التفاسير:

external-link copy
85 : 26

وَٱجۡعَلۡنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ

"Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima." info
التفاسير:

external-link copy
86 : 26

وَٱغۡفِرۡ لِأَبِيٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ

"Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu." info
التفاسير:

external-link copy
87 : 26

وَلَا تُخۡزِنِي يَوۡمَ يُبۡعَثُونَ

"Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su." info
التفاسير:

external-link copy
88 : 26

يَوۡمَ لَا يَنفَعُ مَالٞ وَلَا بَنُونَ

"A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi." info
التفاسير:

external-link copy
89 : 26

إِلَّا مَنۡ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلۡبٖ سَلِيمٖ

"Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki." info
التفاسير:

external-link copy
90 : 26

وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ

Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa. info
التفاسير:

external-link copy
91 : 26

وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِلۡغَاوِينَ

Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku. info
التفاسير:

external-link copy
92 : 26

وَقِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ

Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?" info
التفاسير:

external-link copy
93 : 26

مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلۡ يَنصُرُونَكُمۡ أَوۡ يَنتَصِرُونَ

"Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?" info
التفاسير:

external-link copy
94 : 26

فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ

Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun. info

* Gumãkan, sũ da halakakku mabiyansu. Dukkan mai ɓatarda wani shĩ ne gunki ga mai bin sa halakakke.

التفاسير:

external-link copy
95 : 26

وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ

Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya. info
التفاسير:

external-link copy
96 : 26

قَالُواْ وَهُمۡ فِيهَا يَخۡتَصِمُونَ

Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma, info
التفاسير:

external-link copy
97 : 26

تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

"Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna." info
التفاسير:

external-link copy
98 : 26

إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu. info
التفاسير:

external-link copy
99 : 26

وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلۡمُجۡرِمُونَ

"Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi." info
التفاسير:

external-link copy
100 : 26

فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ

"Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta." info
التفاسير:

external-link copy
101 : 26

وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٖ

"Kuma bã mu da abõki, masõyi." info
التفاسير:

external-link copy
102 : 26

فَلَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةٗ فَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

"Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!" info
التفاسير:

external-link copy
103 : 26

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba. info
التفاسير:

external-link copy
104 : 26

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
105 : 26

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ نُوحٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
106 : 26

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba?" info
التفاسير:

external-link copy
107 : 26

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

"Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce." info
التفاسير:

external-link copy
108 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
109 : 26

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
110 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
111 : 26

۞ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلۡأَرۡذَلُونَ

Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?" info
التفاسير: