የቅዱስ ቁርዓን ይዘት ትርጉም - የሀውሳ ቋንቋ ትርጉም - አቡበከር ጉሚ

የገፅ ቁጥር:close

external-link copy
187 : 3

وَإِذۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَتُبَيِّنُنَّهُۥ لِلنَّاسِ وَلَا تَكۡتُمُونَهُۥ فَنَبَذُوهُ وَرَآءَ ظُهُورِهِمۡ وَٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦ ثَمَنٗا قَلِيلٗاۖ فَبِئۡسَ مَا يَشۡتَرُونَ

Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa* Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye! info

* A cikin wannan akwai gargaɗi ga mãlaman Musulmi, kada su shiga hanyar Yahũdu ta ɓõye ilmin gaskiya, ko kuwa abin da ya sãme su, sũ ma ya sãme su, kuma ya shiga da su mashigarsu. Wãjibi ne akan mãlamai su bãyar da abin da ke hannuwansu na ilmi mai amfãni, mai nũni a kan aikin ƙwarai, kada su ɓõye kõme daga gare shi. Idan sun ɓõye, to, la'anar Allah da malã'iku da ta mutãne zã ta tabbata a kansu, kamar yadda ta tabbata a kan mãlaman Yahũdu.

التفاسير:

external-link copy
188 : 3

لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أَتَواْ وَّيُحِبُّونَ أَن يُحۡمَدُواْ بِمَا لَمۡ يَفۡعَلُواْ فَلَا تَحۡسَبَنَّهُم بِمَفَازَةٖ مِّنَ ٱلۡعَذَابِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi. info
التفاسير:

external-link copy
189 : 3

وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. info
التفاسير:

external-link copy
190 : 3

إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali. info
التفاسير:

external-link copy
191 : 3

ٱلَّذِينَ يَذۡكُرُونَ ٱللَّهَ قِيَٰمٗا وَقُعُودٗا وَعَلَىٰ جُنُوبِهِمۡ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ رَبَّنَا مَا خَلَقۡتَ هَٰذَا بَٰطِلٗا سُبۡحَٰنَكَ فَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta. info
التفاسير:

external-link copy
192 : 3

رَبَّنَآ إِنَّكَ مَن تُدۡخِلِ ٱلنَّارَ فَقَدۡ أَخۡزَيۡتَهُۥۖ وَمَا لِلظَّٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

"Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga Azzãlumai. info
التفاسير:

external-link copy
193 : 3

رَّبَّنَآ إِنَّنَا سَمِعۡنَا مُنَادِيٗا يُنَادِي لِلۡإِيمَٰنِ أَنۡ ءَامِنُواْ بِرَبِّكُمۡ فَـَٔامَنَّاۚ رَبَّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرۡ عَنَّا سَيِّـَٔاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ ٱلۡأَبۡرَارِ

"Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki. info
التفاسير:

external-link copy
194 : 3

رَبَّنَا وَءَاتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَىٰ رُسُلِكَ وَلَا تُخۡزِنَا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ إِنَّكَ لَا تُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

"Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar Alkawari." info
التفاسير: