* Wannan kiyãyewa ya auku a wurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. Watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musu gwargwadon hãli.
* An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari daga wurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu.