Bản dịch ý nghĩa nội dung Qur'an - 豪萨语翻译 - 艾布·伯克尔·珠米

Al'fath

external-link copy
1 : 48

إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا

Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 48

لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka* da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imar Sa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya. info

* Laifin Annabi wanda Allah Ya gãfarta, shĩ ne a lõkacin da ya fãra kiran mutãne zuwa ga bauta wa Allah, Shĩ kaɗai, mãsu bauta wa waɗansu abũbuwa sun ga laifinsa a wannan, sun yi ƙiyayya da shi sabõda haka, har suka yi yãƙi da shi, dõmin tsare ibãdarsu, da al'adunsu, har a lõkacin da Allah Ya bã shi rinjãye bayyananne a kansu, suka gãne amfãnin abin da yake kiran su zuwa gare shi na alheri, suka yãfe laifin da suke zato kuma suka so shi son da bã ya ƙãrewa har Tãshin Ƙiyãma. Wannan ni'imar Allah ce babba ga Annabinsa, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi. Hanya madaidaiciya, ita ce sharĩ'ar da Allah Ya bã shi, wadda ke jan jama'arsa a kan alheri har ya zuwa Tãshin ƙiyãma, kuma su tãshi a cikin alheri mafi girma, matuƙar dai sun bĩ ta, sun yi aiki da ita gwargwadon yadda ya nũna musu ita.

التفاسير:

external-link copy
3 : 48

وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا

Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 48

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِيمَٰنٗا مَّعَ إِيمَٰنِهِمۡۗ وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 48

لِّيُدۡخِلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عِندَ ٱللَّهِ فَوۡزًا عَظِيمٗا

Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 48

وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا

Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su). info
التفاسير:

external-link copy
7 : 48

وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا

Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 48

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 48

لِّتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا

Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice. info
التفاسير: