Bản dịch ý nghĩa nội dung Qur'an - 豪萨语翻译 - 艾布·伯克尔·珠米

Fussilat

external-link copy
1 : 41

حمٓ

Ḥ. M̃. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 41

تَنزِيلٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai. info
التفاسير:

external-link copy
3 : 41

كِتَٰبٞ فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani info
التفاسير:

external-link copy
4 : 41

بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا فَأَعۡرَضَ أَكۡثَرُهُمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Yanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. Sai mafi yawansu suka bijire. Sabõda haka sũ, bã su saurãrãwa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 41

وَقَالُواْ قُلُوبُنَا فِيٓ أَكِنَّةٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ وَفِيٓ ءَاذَانِنَا وَقۡرٞ وَمِنۢ بَيۡنِنَا وَبَيۡنِكَ حِجَابٞ فَٱعۡمَلۡ إِنَّنَا عَٰمِلُونَ

Kuma suka ce: "Zukatanmu nã a cikin kwasfa daga abin da kake Kiran mu zuwa gare shi, kuma a cikin kunnuwanmu akwai wani nauyi, kuma daga tsakaninmu da tsakaninka akwai wani shãmaki. sahõda haka ka yi aiki, lalle mũ mãsu aiki ne." info
التفاسير:

external-link copy
6 : 41

قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَٱسۡتَقِيمُوٓاْ إِلَيۡهِ وَٱسۡتَغۡفِرُوهُۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: "Nĩ mutum kawai ne kamarku, ãnã yin wahayi zuwa gare ni cẽwa abin bautãwarku, abin bautãwa guda ne. Sai ku daidaitu zuwa gare Shi, kuma ku nẽmi gafararSa." Kuma bone ya tabbata ga mãsu yin shirki. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 41

ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

Waɗanda bã su bãyar da zakka, kuma sũ a game da Lãhira su kafirai ne. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 41

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ

Lalle wɗdanda suka yi ĩmãni, Kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bai yankẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 41

۞ قُلۡ أَئِنَّكُمۡ لَتَكۡفُرُونَ بِٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ فِي يَوۡمَيۡنِ وَتَجۡعَلُونَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ ذَٰلِكَ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka ce: "Ashe lalle kũ, haƙĩƙa, kunã kafurta a game da wanda Ya halitta kasã a cikin kwanuka biyu, kuma kunã sanya Masa kĩshiyõyi? Wancan fa, shĩ ne Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
10 : 41

وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ مِن فَوۡقِهَا وَبَٰرَكَ فِيهَا وَقَدَّرَ فِيهَآ أَقۡوَٰتَهَا فِيٓ أَرۡبَعَةِ أَيَّامٖ سَوَآءٗ لِّلسَّآئِلِينَ

Kuma Ya sanya, a cikinta, dũwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, kuma Ya ƙaddara abũbuwan cinta a cikinta a cikin kwanuka huɗu mãsu daidaita, dõmin matambaya. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 41

ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ وَهِيَ دُخَانٞ فَقَالَ لَهَا وَلِلۡأَرۡضِ ٱئۡتِيَا طَوۡعًا أَوۡ كَرۡهٗا قَالَتَآ أَتَيۡنَا طَآئِعِينَ

Sa'an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã "Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas." Suka ce: "Mun zo, munã mãsu ɗã'ã. " info
التفاسير: