* Kisan kuskure bãbu ƙisãsi a cikinsa, sai dai biyan diyya da kuma kaffãra. Amma biyan diyya yana kan dukkan dangin mai kisan, gwargwadon ƙarfin su, shi ɗaya ne daga cikin su. Idan danginsa ba su isa ba, ko kuwa bãbu su, to, sai baitulmãli na Musulmi ya biya. Ana biyan diyya a cikin shekaru huɗu. Ana bãyar da ita ga magãdan wanda aka kashe. Amma kaffãra ita kam a kan mai kisan kawai take a kan tartĩbinta. Wanda ya kashe bãwa bisa kuskure zai biya ƙĩmarsa ga mai shi, kuma ana son ya yi kaffãra.