قۇرئان كەرىم مەنىلىرىنىڭ تەرجىمىسى - ھۇساچە تەرجىمىسى- ئەبۇبەكرى جومىي

Al'takweer

external-link copy
1 : 81

إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ

Idan rãna aka shafe haskenta info
التفاسير:

external-link copy
2 : 81

وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ

Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani). info
التفاسير:

external-link copy
3 : 81

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ

Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 81

وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ

Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba. info

* Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.

التفاسير:

external-link copy
5 : 81

وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ

Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 81

وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ

Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 81

وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ

Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu. info

* Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.

التفاسير:

external-link copy
8 : 81

وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ

Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta. info

* A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.

التفاسير:

external-link copy
9 : 81

بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ

"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?" info
التفاسير:

external-link copy
10 : 81

وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ

Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su). info
التفاسير:

external-link copy
11 : 81

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ

Kuma idan sama aka fẽɗe ta. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 81

وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ

Kuma idan Jahĩm aka hũra ta info
التفاسير:

external-link copy
13 : 81

وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ

Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 81

عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ

Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan). info
التفاسير:

external-link copy
15 : 81

فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ

To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba. info

* Masu tafiya suna kõmawa bãya.

التفاسير:

external-link copy
16 : 81

ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ

Mãsu gudu suna ɓũya. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 81

وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ

Da dare idan ya bãyar da bãya. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 81

وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ

Da sãfiya idan ta yi lumfashi. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 81

إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ

Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 81

ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ

Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 81

مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ

Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 81

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ

Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 81

وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ

Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani. info

* Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.

التفاسير:

external-link copy
24 : 81

وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ

Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne. info

* Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.

التفاسير:

external-link copy
25 : 81

وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ

Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 81

فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ

Shin, a inã zã ku tafi? info
التفاسير:

external-link copy
27 : 81

إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 81

لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ

Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 81

وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda. info
التفاسير: