Traduzione dei Significati del Sacro Corano - Traduzione hausa - Abubakar Gomi
Al'takweer
1:81
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
Idan rãna aka shafe haskenta
التفاسير:
2:81
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
التفاسير:
3:81
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
التفاسير:
4:81
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
* Rãƙuma mãsu ciki ɗan wata gõma.
التفاسير:
5:81
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
التفاسير:
6:81
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
التفاسير:
7:81
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu.
* Ko kuma, aka haɗa kõwane mutum da irin mutãnensa a Aljanna ko a wuta.
التفاسير:
8:81
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ
Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta.
* A cikin zãmanin jahiliyya Lãrabãwa bã su son a haifa musu 'ya'ya mãta dõmin haka har sukan turbuɗe 'ya'yansu dõmin kada su yi abin kunya ko kuma su talauce wajen yi musu aure.
التفاسير:
9:81
بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ
"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
التفاسير:
10:81
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
التفاسير:
11:81
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ
Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
التفاسير:
12:81
وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
التفاسير:
13:81
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
التفاسير:
14:81
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
التفاسير:
15:81
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba.
* Masu tafiya suna kõmawa bãya.
التفاسير:
16:81
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
Mãsu gudu suna ɓũya.
التفاسير:
17:81
وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
Da dare idan ya bãyar da bãya.
التفاسير:
18:81
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
التفاسير:
19:81
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
التفاسير:
20:81
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
التفاسير:
21:81
مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
التفاسير:
22:81
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
التفاسير:
23:81
وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ
Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani.
* Annabi ya ga Mala'ika Jibirilu ya san shi. Sabõda haka wani aljani bã zai yi kama da shi ba balle ya kãwo masa ƙarya.
التفاسير:
24:81
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ
Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne.
* Ma'anar gaibi a nan, ilmin da Allah Ya aiko Jibirilu da shi zuwa ga Annabi Annabi ba ya ɓõye shi daga mutãne. Ga wata ƙira'a, wanda ake tuhuma, wãto ba a tuhumar Annabi, ga gaibin da ya faɗi cewa daga Allah yake, wato Alƙur'ãni duka gaskiya ne.
التفاسير:
25:81
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
التفاسير:
26:81
فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ
Shin, a inã zã ku tafi?
التفاسير:
27:81
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.