قۇرئان كەرىم مەنىلىرىنىڭ تەرجىمىسى - ھۇساچە تەرجىمىسى- ئەبۇبەكرى جومىي

بەت نومۇرى:close

external-link copy
103 : 37

فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ

Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago info
التفاسير:

external-link copy
104 : 37

وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ

Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" info
التفاسير:

external-link copy
105 : 37

قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
106 : 37

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ

Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. info
التفاسير:

external-link copy
107 : 37

وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ

Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
108 : 37

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ

Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. info
التفاسير:

external-link copy
109 : 37

سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ

Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. info
التفاسير:

external-link copy
110 : 37

كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
111 : 37

إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. info
التفاسير:

external-link copy
112 : 37

وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ

Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. info

* Wannan sãbuwar bushãra da Is'hãƙa tanã nũna cewa bã shĩ ne wanda kissar yankã ta shãfa ba sabõda haka Isma'ĩla dai ne tabbas, mai ƙissar yankã. Sabõda haka Allah Ya sanya shi wata al'umma dabam' dõmin a sãka masa, sa'an nan aka sãkawa Ibrãhĩm da Is'hãƙa dõmin ya zama wata al'umma ta dabam,.

التفاسير:

external-link copy
113 : 37

وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ

Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). info
التفاسير:

external-link copy
114 : 37

وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. info
التفاسير:

external-link copy
115 : 37

وَنَجَّيۡنَٰهُمَا وَقَوۡمَهُمَا مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ

Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. info
التفاسير:

external-link copy
116 : 37

وَنَصَرۡنَٰهُمۡ فَكَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ

Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. info
التفاسير:

external-link copy
117 : 37

وَءَاتَيۡنَٰهُمَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلۡمُسۡتَبِينَ

Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. info
التفاسير:

external-link copy
118 : 37

وَهَدَيۡنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. info
التفاسير:

external-link copy
119 : 37

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِمَا فِي ٱلۡأٓخِرِينَ

Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. info
التفاسير:

external-link copy
120 : 37

سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. info
التفاسير:

external-link copy
121 : 37

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
122 : 37

إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai. info
التفاسير:

external-link copy
123 : 37

وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
124 : 37

إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" info
التفاسير:

external-link copy
125 : 37

أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ

"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" info
التفاسير:

external-link copy
126 : 37

ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ

"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" info
التفاسير: