قۇرئان كەرىم مەنىلىرىنىڭ تەرجىمىسى - ھۇساچە تەرجىمىسى- ئەبۇبەكرى جومىي

Al'safat

external-link copy
1 : 37

وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفّٗا

Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). info
التفاسير:

external-link copy
2 : 37

فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا

Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi. info

* Mãsu tsãwa, sũ ne Malamai mãsu sãmun ilmin wa'azi daga Annabãwa waɗanda ke karãtun abin tunãwa daga Allah Ubangijin sammai da ƙasa, Mai bãyar da haske ga rãnã, Mai haskaka taurari mãsu ƙãwãtar da samã kuma su tsare ta daga shaiɗanu. An siffanta rãnã da Annabãwa, Malamai da taurãri, ilmi da haske da sababin ƙawa da shiryarwa da kõrar mãsu ɓarna.

التفاسير:

external-link copy
3 : 37

فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا

Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 37

إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ

Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 37

رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 37

إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ

Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 37

وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ

Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 37

لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ

Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 37

دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ

Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 37

إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ

Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 37

فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٖ لَّازِبِۭ

Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 37

بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ

Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 37

وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ

Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 37

وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةٗ يَسۡتَسۡخِرُونَ

Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 37

وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٌ

Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." info
التفاسير:

external-link copy
16 : 37

أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ

"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? info
التفاسير:

external-link copy
17 : 37

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ

"Ashe kõ da ubanninmu na farko?" info
التفاسير:

external-link copy
18 : 37

قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ

Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." info
التفاسير:

external-link copy
19 : 37

فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ

Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 37

وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ

Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." info
التفاسير:

external-link copy
21 : 37

هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. info
التفاسير:

external-link copy
22 : 37

۞ ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ

Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. info
التفاسير:

external-link copy
23 : 37

مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ

Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 37

وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ

Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. info
التفاسير: