* Mutãnensa mũminai. Ĩmãni da gaskiya idan gaskiya ta bayyana asĩri ne daga asĩran Allah sai wanda Ya bai wa. Kusanci ga wani Annabi da aure kõ zumunta, bã ya bãyar da shi. Ruwan azãba, shĩ ma asĩri ne na Allah.
* Daga wannan ãyã ta 59 zuwa ƙarshen Sũra, duka tambĩhi ne ga abũbuwan fake na ilmin Allah, wanda ya shãfi jikunanmu, amma ba mu san yadda suke aukuwa a gare mu ba. Sa'an nan kuma da tambĩhi ga abũbuwan gaibi da suke zuwa dõmin mu yi ĩmãni da su.