Përkthimi i kuptimeve të Kuranit Fisnik - Përkthimi në gjuhën hausa - Ebubekër Xhumi

Al'insan

external-link copy
1 : 76

هَلۡ أَتَىٰ عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ حِينٞ مِّنَ ٱلدَّهۡرِ لَمۡ يَكُن شَيۡـٔٗا مَّذۡكُورًا

Lalle ne, wata mudda ta zamani tã zo a kan mutum, bai kasance kõme ba wanda ake ambata. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 76

إِنَّا خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٍ أَمۡشَاجٖ نَّبۡتَلِيهِ فَجَعَلۡنَٰهُ سَمِيعَۢا بَصِيرًا

Lalle ne, Mũ Mun halitta mutum daga ɗigon ruwa garwayayye, Muna jarraba shi, sabõda haka Muka sanya shi mai ji mai gani, info
التفاسير:

external-link copy
3 : 76

إِنَّا هَدَيۡنَٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرٗا وَإِمَّا كَفُورًا

Lalle ne, Mũ, Mun shiryar da shi ga hanyar ƙwarai, ko ya zama mai gõdiya, kuma ko ya zama mai kãfirci. info
التفاسير:

external-link copy
4 : 76

إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَلَٰسِلَاْ وَأَغۡلَٰلٗا وَسَعِيرًا

Lalle ne, Mũ, Mun yi tattali, dõmin kãfirai, sarƙoƙi da ƙuƙumma da sa'ĩr. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 76

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ يَشۡرَبُونَ مِن كَأۡسٖ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا

Lalle ne, mutãnen kirki zã su sha daga finjãlin giya abin gaurayarta yã kãsance kãfur ne. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 76

عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا عِبَادُ ٱللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفۡجِيرٗا

Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 76

يُوفُونَ بِٱلنَّذۡرِ وَيَخَافُونَ يَوۡمٗا كَانَ شَرُّهُۥ مُسۡتَطِيرٗا

Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 76

وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا

Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 76

إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمۡ جَزَآءٗ وَلَا شُكُورًا

(Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 76

إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوۡمًا عَبُوسٗا قَمۡطَرِيرٗا

"Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa." info
التفاسير:

external-link copy
11 : 76

فَوَقَىٰهُمُ ٱللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمِ وَلَقَّىٰهُمۡ نَضۡرَةٗ وَسُرُورٗا

Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki, info
التفاسير:

external-link copy
12 : 76

وَجَزَىٰهُم بِمَا صَبَرُواْ جَنَّةٗ وَحَرِيرٗا

Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 76

مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۖ لَا يَرَوۡنَ فِيهَا شَمۡسٗا وَلَا زَمۡهَرِيرٗا

Sunã mãsu zaman ginciri,* a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura. info

* Kishingiɗa.

التفاسير:

external-link copy
14 : 76

وَدَانِيَةً عَلَيۡهِمۡ ظِلَٰلُهَا وَذُلِّلَتۡ قُطُوفُهَا تَذۡلِيلٗا

Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 76

وَيُطَافُ عَلَيۡهِم بِـَٔانِيَةٖ مِّن فِضَّةٖ وَأَكۡوَابٖ كَانَتۡ قَوَارِيرَا۠

Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 76

قَوَارِيرَاْ مِن فِضَّةٖ قَدَّرُوهَا تَقۡدِيرٗا

¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 76

وَيُسۡقَوۡنَ فِيهَا كَأۡسٗا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا

Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 76

عَيۡنٗا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلۡسَبِيلٗا

Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 76

۞ وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيۡتَهُمۡ حَسِبۡتَهُمۡ لُؤۡلُؤٗا مَّنثُورٗا

Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa. info
التفاسير:

external-link copy
20 : 76

وَإِذَا رَأَيۡتَ ثَمَّ رَأَيۡتَ نَعِيمٗا وَمُلۡكٗا كَبِيرًا

Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba. info
التفاسير:

external-link copy
21 : 76

عَٰلِيَهُمۡ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضۡرٞ وَإِسۡتَبۡرَقٞۖ وَحُلُّوٓاْ أَسَاوِرَ مِن فِضَّةٖ وَسَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ شَرَابٗا طَهُورًا

Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki). info
التفاسير:

external-link copy
22 : 76

إِنَّ هَٰذَا كَانَ لَكُمۡ جَزَآءٗ وَكَانَ سَعۡيُكُم مَّشۡكُورًا

(A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa." info
التفاسير:

external-link copy
23 : 76

إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ تَنزِيلٗا

Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa. info
التفاسير:

external-link copy
24 : 76

فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعۡ مِنۡهُمۡ ءَاثِمًا أَوۡ كَفُورٗا

Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci. info
التفاسير:

external-link copy
25 : 76

وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا

Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice. info
التفاسير:

external-link copy
26 : 76

وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَٱسۡجُدۡ لَهُۥ وَسَبِّحۡهُ لَيۡلٗا طَوِيلًا

Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo. info
التفاسير:

external-link copy
27 : 76

إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ يُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَآءَهُمۡ يَوۡمٗا ثَقِيلٗا

Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi. info
التفاسير:

external-link copy
28 : 76

نَّحۡنُ خَلَقۡنَٰهُمۡ وَشَدَدۡنَآ أَسۡرَهُمۡۖ وَإِذَا شِئۡنَا بَدَّلۡنَآ أَمۡثَٰلَهُمۡ تَبۡدِيلًا

Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa. info
التفاسير:

external-link copy
29 : 76

إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا

Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa. info
التفاسير:

external-link copy
30 : 76

وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima. info
التفاسير:

external-link copy
31 : 76

يُدۡخِلُ مَن يَشَآءُ فِي رَحۡمَتِهِۦۚ وَٱلظَّٰلِمِينَ أَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمَۢا

Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi. info
التفاسير: