* Mijin zai fita ya bar wa mãtar da ya saki ɗaki ta zauna a ɗakinta har ta ƙãre idda. Anã ciyar da mai sakin kõme, amma bã a ciyar da mai sakin bã'ini sai idan tanã da ciki. Ijãrar shãyarwa tanã akan uba ga uwar da aka saki saki bã'ini kõ ga watarta, bisa ga yardar sassan biyu.
* A bãyan da ya gama bayãnin saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce-hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cewa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce-hukuncen Sa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuwa ga hasken sharĩ'ar Sa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtar Sa mai yawa.
* Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: "Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki," bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.