* Faɗarsu ta izgili watau suna cewa: "Mun kashe ĩsã ɗan Maryama wanda yake da'awar shi Manzon Allah ne." Asalin maganar Yahũdu suka karkatar da Dãwũda sarkin Dimashƙa, da cewa ga wani mutum nan yana ɓãta ƙasa da aƙĩdar mutãne a Baitil Maƙdis sabõda haka ya bãyar da õda ga hãkimansa a Baitil Maƙdis da a kashe ĩsã sai suka tafi suka tsare shi a cikin gida shi da sahabbansa, watau Hawãriyawa. ĩsã ya rõki waninsu da yarda da kisa a kan sakamakon Aljanna. Sai ƙaraminsu ya yarda, Allah Ya sanya masa sifar ĩsã, a bãyan haka Ya ɗauke ĩsã. Shi kuma aka kashe shi matsayin ĩsã. Daga nan,Yahũdu suna zaton sun kashe shi, kuma waɗanda suka halarci ƙissar, suka sãɓã wa jũna wajen sifar ĩsã da cewa Shi ne Allah, ko ɗan Allah, ko ɗayan uku, ko manzon Allah, kamar yadda ya gabãta a cikin Baƙara.
* An ce Mutãnen Littafi na zamanin Annabi Isa lalle suna imani da shi gabanin mutuwarsa cewa shi ba Allah ne ba, kuma ba ɗan Allah ne ba; kowannensu kamin ya mutu yana imani da cewa Isa Manzon A1lah ne, a lokacin da imanin ba ya amfanin sa. Allah Ya fi sani.
* Kabĩla mai asali tana lãlãcewa sabõda rashin bin addini, har ta zama mafi sharrin halittar Allah, kamar Yahũdu. Kuma a cikin haka wanda ya komawa gaskiya sai ya koma ga tsohon asalin, ya ƙãra daukaka da shi, kamar waɗanda suka musulunta daga cikinsu.