* Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.
* Gulũlu shĩ ne satar wani abu daga ganimar yãƙi a gabãnin raba ta a tsakãnin mayãka. Allah Yã ce, "Yin gulũlu haram ne a kan kõwane annabi ko da waɗanda ba a halatta wa cin ganima ba, balle ga wanda aka halatta wa. Kamar yadda gulũlu yake haram a kan annabãwa haka yake haram a kan mabiyansu.".
* Mũminai mãsu darajõji ne a wurin Allah gwargwadon ĩmãninsu da taƙawarsu da kuma falalar da Allah Ya yi musu. Haka sũ kuma kãfirai sunã da magangara zuwa ƙasa gwargwadon mugun aikinsu.
* Allah Yã nũna falalar da Ya bai wa Annabi Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da yake har yanã yi wa mũminai gõri da kyautar da Ya yi musu ta hanyar aiko musu shi.
* Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓãwa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alheri biyu sun sãme ku. ** Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka.