Përkthimi i kuptimeve të Kuranit Fisnik - Përkthimi në gjuhën hausa - Ebubekër Xhumi

Numri i faqes:close

external-link copy
112 : 26

قَالَ وَمَا عِلۡمِي بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa." info
التفاسير:

external-link copy
113 : 26

إِنۡ حِسَابُهُمۡ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّيۖ لَوۡ تَشۡعُرُونَ

"Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa." info
التفاسير:

external-link copy
114 : 26

وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

"Ban zama mai kõre mũminai ba." info
التفاسير:

external-link copy
115 : 26

إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ

"Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa." info
التفاسير:

external-link copy
116 : 26

قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ

Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa" info
التفاسير:

external-link copy
117 : 26

قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ

Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni." info
التفاسير:

external-link copy
118 : 26

فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحٗا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

"Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai." info
التفاسير:

external-link copy
119 : 26

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ

Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi. info
التفاسير:

external-link copy
120 : 26

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ

Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran. info
التفاسير:

external-link copy
121 : 26

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba. info
التفاسير:

external-link copy
122 : 26

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama. info
التفاسير:

external-link copy
123 : 26

كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni. info
التفاسير:

external-link copy
124 : 26

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ

A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?" info
التفاسير:

external-link copy
125 : 26

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

"Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce." info
التفاسير:

external-link copy
126 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
127 : 26

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

"Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu." info
التفاسير:

external-link copy
128 : 26

أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ

"Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?" info

* Sitãdiyo shi ne gidan wasanni da Turanci, alãmã da Lãrabci.

التفاسير:

external-link copy
129 : 26

وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ

"Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?*" info

* Kõ kuma wurãren sanã'õ'i kamar masãƙoƙi irin na zãmanin nan.

التفاسير:

external-link copy
130 : 26

وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ

"Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa." info
التفاسير:

external-link copy
131 : 26

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

"To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã." info
التفاسير:

external-link copy
132 : 26

وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ

"Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani." info
التفاسير:

external-link copy
133 : 26

أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ

"Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya." info
التفاسير:

external-link copy
134 : 26

وَجَنَّٰتٖ وَعُيُونٍ

"Da gõnaki da marẽmari." info
التفاسير:

external-link copy
135 : 26

إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

"Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma." info
التفاسير:

external-link copy
136 : 26

قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ

Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba." info
التفاسير: