Vertaling van de betekenissen Edele Qur'an - Hausa vertaling - Abu Bakr Jumi

Alkiyama

external-link copy
1 : 75

لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ

Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba. info

* Wasu na fassarawa: lna rantsuwa da Rãnar Ƙiyama. A ganina, da tabbatar da rantsuwar da kuma kore ta duka ɗaya ne, maƙasũdi dai jan hankalin mai karãtu ga abin da yake a ciki, na hikimar Allah.

التفاسير:

external-link copy
2 : 75

وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ

Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba. info

* Kowane rai na zargin kansa idan bai yi aikin alheri ba, ko kuma bai yi fiye da wanda ya yi ba, ko kuma bai aikata wanda ya fi kyãwo ba a lokacin aikinsa.

التفاسير:

external-link copy
3 : 75

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ

Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? info
التفاسير:

external-link copy
4 : 75

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ

Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 75

بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ

Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. info
التفاسير:

external-link copy
6 : 75

يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ

Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" info
التفاسير:

external-link copy
7 : 75

فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ

To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). info
التفاسير:

external-link copy
8 : 75

وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ

Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). info
التفاسير:

external-link copy
9 : 75

وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ

Aka tãra rãnã da watã info
التفاسير:

external-link copy
10 : 75

يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ

Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" info
التفاسير:

external-link copy
11 : 75

كَلَّا لَا وَزَرَ

A'aha! bãbu mafaka. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 75

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ

zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. info
التفاسير:

external-link copy
13 : 75

يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ

Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 75

بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ

Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 75

وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ

Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). info
التفاسير:

external-link copy
16 : 75

لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ

Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). info

* Dangantakar wannan ãya da ta sama da ita, ita ce bambancin Annabi mai gaggawar karɓar umurnin Allah da ƙyamar kãfiri ga karɓarsa, da bayãnin sauƙaƙewar Allah ga mai bin umurninSa.

التفاسير:

external-link copy
17 : 75

إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ

Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. info
التفاسير:

external-link copy
18 : 75

فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ

To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. info
التفاسير:

external-link copy
19 : 75

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ

sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. info
التفاسير: