Vertaling van de betekenissen Edele Qur'an - Hausa vertaling - Abu Bakr Jumi

Pagina nummer:close

external-link copy
10 : 3

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَن تُغۡنِيَ عَنۡهُمۡ أَمۡوَٰلُهُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُهُم مِّنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗاۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمۡ وَقُودُ ٱلنَّارِ

Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu bã su tunkuɗe musu kõme daga Allah, kuma 'ya'yansu bã su tunkuɗẽwa, kuma waɗannan, sũ ne makãmashin wuta. info
التفاسير:

external-link copy
11 : 3

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kamar ɗabi'ar mutãnen Fir'auna da waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata ãyõyinMu, sai Allah Ya kãmã su sabõda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 3

قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ سَتُغۡلَبُونَ وَتُحۡشَرُونَ إِلَىٰ جَهَنَّمَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Ka ce wa waɗanda suka kãfirta: "Za a rinjãye ku, kuma a tãraku zuwa Jahannama, kuma shimfiɗar tã mũnana! info
التفاسير:

external-link copy
13 : 3

قَدۡ كَانَ لَكُمۡ ءَايَةٞ فِي فِئَتَيۡنِ ٱلۡتَقَتَاۖ فِئَةٞ تُقَٰتِلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَأُخۡرَىٰ كَافِرَةٞ يَرَوۡنَهُم مِّثۡلَيۡهِمۡ رَأۡيَ ٱلۡعَيۡنِۚ وَٱللَّهُ يُؤَيِّدُ بِنَصۡرِهِۦ مَن يَشَآءُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ

"Lalle ne wata ãyã tã kasance a gare ku a cikin ƙungiyõyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yãƙi a cikin hanyar Allah, da wata kãfira, suna ganin su ninki biyu nãsu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakĩƙa, akwai abin kula ga maabũta basĩra. info
التفاسير:

external-link copy
14 : 3

زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ

An ƙawata wa mutãne son sha'awõyi daga mãtã da ɗiya da dũkiyõyi abũbuwan tãrãwa daga zinariya da azurfa, da dawãki kiwãtattu da dabbõbin ci da hatsi. Wannan shi ne dãɗin rãyuwar dũniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyãwar makõma take. info
التفاسير:

external-link copy
15 : 3

۞ قُلۡ أَؤُنَبِّئُكُم بِخَيۡرٖ مِّن ذَٰلِكُمۡۖ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَأَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alhẽri daga wannan? Akwai gidãjen Aljanna a wurin Ubangiji sabõda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, kõguna suna gudãna daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da mãtan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bãyinSa. info
التفاسير: