* Bãyan kiran mutãne gabã ɗaya zuwa ga addinin musulunci, sai kuma ya keɓance Yahũdu da kira zuwa ga addinin, dõmin sun bambanta da sauran kãfirai, sabõda ilminsu ga gaskiyar Musulunci. Yã gabata cewa jama'ar, kashi huɗu ce; mũminai, da kãfiran Lãrabãwan da bã zã su musulunta ba, da munãfukai da Yahũdu. Ya kira Yahũdu da Bani Isrã'ĩla, dõmin Ya tunãtar da su, cewa anã kiransu ne zuwa ga addini irin na ubansu Ya'aƙũbu bawan Allah.