* Bayãnin hukuncin tsare lõkutan salla a cikin kõwane hãli: aminci ko tsõro, da bãyar da salla yadda hãli ya bãyar duka; tsaye kõ da tafiya kõ gudãne. Hikimar sanya wannan hukunci a tsakãnin hukunce-hukuncen aure dõmin farkarwa a kan muhimmancin salla, dõmin kada mu'ãmala ta shagaltar da Musulmi daga gare ta.
* Al'ãda idan ba ta sãɓã wa rukunin sharĩ'a ba bã a hana ta sai dai bãbu tilastãwa ga yinta. A zamanin Jãhiliyya mãtã suna iddar mutuwar mazansu shekara guda. Wanda ya yi wasiyyar kada matarsa ta fita daga ɗãkinta har shekara ana karɓar masa sai dai bãbu tĩlas a gare ta da ta zauna, dõmin an shãfe hukuncin iddar shekara ta al'ãdar Jãhiliyya.
* Bayãnin hukuncin dãɗaɗãwa ga mãtan da aka saki bãyan an yi zaman aure da su Tamattu'i gare su wãjibi ne a kan mazansu, gwargwadon hãli.
* Wasu mutãne ne daga cikin Bani Isrã'ila annõba tã auku a kansu sai suka fita daga gidãjensu dõmin gudun mutuwa sũ dubũ huɗu kõ takwas kõ wanin wannan adadi, sai Allah Ya ce musu; "Ku mutu,"sai suka mutu kwana takwas kõ fiye da haka. Sa'an nan kuma Allah Ya tãyar da su dõmin Ya nũna musu cewa gudun mutuwa, bã ya hana ta, sai abin da Ya so, shi ke aukuwa. Wannan ƙissa tanã amfãnar da ƙarfafa rãyuka dõmin jihãdi, sabõda haka umurni da yãƙi ya bĩ ta; watau ita shimfiɗa ce ga umurnin jihãdi da fita zuwa yãƙi. Kuma sũrar na karantar da tattalin arziki daga nan zuwa ƙarshenta. Watau kafa gari wajibi ne ga tattalin arziki.
* Bãyãni ga cewa jihãdi bã ya yiwuwa sai mutãne kõwa ya bãyar da taimakonsa na dũkiya kõ na ma'ana. Kuma duk wanda ya bãyar da taimako, to, rance ne ya bai wa Allah, Wanda yake Shi ne Ya bãyar da asalin dũkiyar, da yawa kõ kaɗan, kuma Mai sakamako ga wanda ya yi aiki da umurninSa da babban sakamako, bãyan an kõma zuwa gareShi. Jihãdi wãjibi ne ga tattalin arziki domin tsaro.