クルアーンの対訳 - ハウサ語対訳 - Abu Bakr Jomy

Al'dariq

external-link copy
1 : 86

وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ

Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare. info
التفاسير:

external-link copy
2 : 86

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ

To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare? info
التفاسير:

external-link copy
3 : 86

ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ

Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.* info

* Wannan ya yi kama da zuwan Annabi a cikin jahiliyya don ya haskaka duniya da ilimi kamar yadda girgije ke ba da ruwa saboda tsiron ƙasa, hantsar uwa ta ba da nono saboda jariri kuma maniyi ya zo lokacin Jima'i.

التفاسير:

external-link copy
4 : 86

إِن كُلُّ نَفۡسٖ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٞ

Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro. info
التفاسير:

external-link copy
5 : 86

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ

To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi? info
التفاسير:

external-link copy
6 : 86

خُلِقَ مِن مَّآءٖ دَافِقٖ

An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. info
التفاسير:

external-link copy
7 : 86

يَخۡرُجُ مِنۢ بَيۡنِ ٱلصُّلۡبِ وَٱلتَّرَآئِبِ

Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji. info
التفاسير:

external-link copy
8 : 86

إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٞ

Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne. info
التفاسير:

external-link copy
9 : 86

يَوۡمَ تُبۡلَى ٱلسَّرَآئِرُ

Rãnar da ake jarrabawar asirai. info
التفاسير:

external-link copy
10 : 86

فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٖ وَلَا نَاصِرٖ

Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah). info
التفاسير:

external-link copy
11 : 86

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجۡعِ

Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa. info
التفاسير:

external-link copy
12 : 86

وَٱلۡأَرۡضِ ذَاتِ ٱلصَّدۡعِ

Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,* info

* Dõmin fitar tsiro.

التفاسير:

external-link copy
13 : 86

إِنَّهُۥ لَقَوۡلٞ فَصۡلٞ

Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki* info

* Mai rabewa tsakanin ƙarya da gaskiya.

التفاسير:

external-link copy
14 : 86

وَمَا هُوَ بِٱلۡهَزۡلِ

Kuma shĩ bã bananci* bane info

* Kãkãci.

التفاسير:

external-link copy
15 : 86

إِنَّهُمۡ يَكِيدُونَ كَيۡدٗا

Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai. info
التفاسير:

external-link copy
16 : 86

وَأَكِيدُ كَيۡدٗا

Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi. info
التفاسير:

external-link copy
17 : 86

فَمَهِّلِ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَمۡهِلۡهُمۡ رُوَيۡدَۢا

Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu. info
التفاسير: